Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Najeriya a Nijar Sun Bayyana Ra'ayoyinsu Kan Zabin Ministocin Buhari


Shugaba Buhari Buhari da Sanata Bukola Saraki shugaban majalisar dattawa, majalisar da zata tantance sabbin ministocin da za'a nada

Muryar Amurka ta bi wasu 'yan Najeriya mazauna Jamhuriyar Nijar saboda jin ra'ayoyinsu akan mutanen da Buhari ya zaba su zama ministocinsa.

‘Yan najeriya mazauna Nijer sun tofa albarkacinsu a game da sunayen mutanen da shugaba MUAMMADU BUHARI ya aikewa majalisar dattawa domin tantancewa kafin a nada su ministoci a sabuwar gwamnatin da yaka kafawa.

Kusan ana iya cewa wannan magana ta jerin sunayen da shugaba Buhari ya aikewa majalisar dattawan Najeriya domin tantancewa kafin a basu mikamin minista ita ce maganar dake daukar hankalin ‘yan Najeriya mazauna Nijer a yanzu haka. Wadanda Muryar Amurka ta tunutuba sun bayyana gamsuwa da zabin na Muhammadu Bukari.

A dangane da rashin saka matasa a shirin kafa sabuwar gwamnatin tashi ‘yan Najeriya mazaunan Nijer na ganin lokacin ba matasa mukaman gwamnatin tarayya bai yi ba.

Ga wadanda majalisardattawaza ta amincewa shigarsu cikin sabuwar gwamnatin da APC ta kafawatanni kusan 6 bayan lashe zabe ‘yan Najeriyana gargadinsu da su kasance masu rikon amana tare da kawar da duk wasu bambance bambancen addini ko na kabila ko kuma na bangaranci.

Ga karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:32 0:00

XS
SM
MD
LG