Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan sanda a jamhuriyar Benin sunyi amfani da barkonon tsohuwa akan masu zanga-zangar


'Yan sanda a jamhuriyar Benin sunyi amfani da barkonon tsohuwa akan masu zanga-zangar

Jiya alhamis ‘yan sanda a Jamhuriyar Benin suka yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa ‘yan zanga-zangar dake nuna rashin jin dadin sake zaben shugaba Boni yayi da aka yi a wa’adi na biyu a zaben ranar 13 ga watan nan na Maris.

Jiya alhamis ‘yan sanda a Jamhuriyar Benin suka yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa ‘yan zanga-zangar dake nuna rashin jin dadin sake zaben shugaba Boni yayi da aka yi a wa’adi na biyu a zaben ranar 13 ga watan nan na Maris. Masu zanga-zangar sun hallara Cotonou, cibiyar kasuwanci ta kasar, wasu dauke da kwalaye su na ikirarin nuna goyon bayan shugaban hamayya Adrien Houngbedji. Wani baturen ‘yan sanda ya fadawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa masu zanga-zangar sun kona tayu suka kuma toshe hanya a wasu wurare biyu. ‘Yan hamayya sun yi zargin cewa an tabka magudi a zaben. A ranar litinin, kotun tsarin mulki ta Jamhuriyar Benin ta tabbatar da sahihancin sakamakon da ya nuna Mr. Yayi ya samu kashi 53 cikin 100, shi kuma Houngbedji ya zo na biyu da kashi 36 cikin 100. Kungiyar tarayyar Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma, ECOWAS ko CEDEAO ta ce duk da wasu kananan matsalolin da aka samu, an gudanar da wannan zabe ba tare da ha’inci ba. An jinkirta gudanar da zaben har sau biyu a saboda matsalolin kayan aiki.

XS
SM
MD
LG