Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Siyasan Nijar Na Ganin Kabila Na Dimkradiyar Congo Ya Wuce Gona da Iri


Joseph Kabila na Dimokradiyar Congo wanda wa'adin mulkinsa ya kare ranar Litinin da ta gabata amma ya ki mika mulki

Ranar Litinin din nan da ta gabata ya kamata shugaban kasar Dimokradiyar Congo ya bar mulki ya mikawa firayim ministan kasar har sai an yi sabon zaben shugaban kasa amma ya yiwa zaben zagon kasa can baya domin ya cigaba da rike da mulki bayan karewar wa'adinsa

Masu sharhi a Nijar na ganin takaddamar neman mulki a kasar Dimokradiyar Congo ba bakon abu ba ne idan aka yi la'akari da cewa akasarin shugabannin da suka kulketa sun hau karagar mulki ne ta haramtacciyar hanya.

Tun daga Mobutu zuwa mahaifin mai ci yanzu wato Lawrenca Kabila da shi kansa Joseph Kabila wanda yanzu ya ki barin mulki. Amma 'yan siyasar Nijar na ganin a wannan lokacin Shugaba Joseph Kabila ya wuce gona da iri.

Alhaji Tahiru Gimba dan takarar shugaban kasa a karkashin tutar jam'iyyar MODEL Ma'aikata a zaben 2016 ya nuna takaicinsa akan yadda shugabannin Afirka ke son mayarda mulki tamkar abun gado. Yace da zara sun hau karagar mulki sai su soma mulkin kama karya. Basu yiwa kasarsu aiki sai kula da kansu da iyalansu tare da yin sata saboda haka sauka daga mulki sai yayi wuya. Kamata yayi idan wa'adin mutum ya cika ya tara kayansa ya tafi.

Kungiyoyin rajin kare dimokradiya sun ce rashin kishin kasa shi yasa wasu shugabannin ke rungumar hanyoyin da zasu basu damar dawama a kan mulki ko ta halin yaya.

Joli Ibrahim na wata kungiya yace lokacin Kabila ya kare kuma kowa ya san ba'a yi zabe ba ya zama tarkon da zai iya tsunduma kasar cikin wani mawuyacin hali. Yace kasar bata taba samun kwanciyar hankali ba.Kasa ce mai arziki amma ta rasa shugabanni nagari. Yace yawancin shugabannin Afirka basa wani aiki sai zalunci da danniya.

Shugaban MODEL ya cigaba da cewa talakawa ne ke da maganin shugabanni masu nacewa kujerar mulki kamar yadda lamarin ya faru a shekarar 2009 a Nijar. Haka ma talakawa suka kori Campaore daga mulki a Burkina Faso a shekarar 2014.

A shekarar 2001 ne Joseph Kabila ya dare kan karagar mulki bayan rasuwar mahaifinsa Lawrence Kabila wanda ya kwashe fiye da shekaru goma yana mulkin da ya kwace daga hannun Mobutu. Shi ma Lawrence Kabila din kasheshi aka yi

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG