Accessibility links

Shugaban Kasar Libya Yace 'yan ta'adda ke da alhakln harin da ya yi sanadin kashe jakaden Amurka


Firai Ministan Libya Abdurrahim El-Keib a hagu da shugaban kasar President Mohammed el-Magarief
Shugaban kasar Libya yace harin da ya kashe jakadan Amurka Christopher Stevens da wasu ma’aikatan jakadanci uku a karamin ofishin jakadancin Amurka dake birnin Benghazi, harin ta’addanci ne da aka tsara tun kafin ranar.

A cikin hirar da yayi yau laraba da gidan telebijin na NBC News na nan Amurka, shugaba Mohammed el-Magarief, yace wannan harin ba ya da nasaba ko kadan da zanga-zangar da aka yi ta nuna kin jinin wani bidiyo na batunci ga addinin Musulunci.

A baya cikin wannan watan ma, jami’an Amurka sun bayyana harin a zaman na ta’addanci. An kai farmakin ne a ranar tunawa da hare-haren ta’addancin da aka kai kan Amurka ranar 11 ga watan Satumbar 2001.

Wannan lamarin ya faru a daidai lokacin da dubban Musulmi suke zanga-zangar nuna rashin jin dadin wani fim da wani mutumin da ya tsani addinin Musulunci ya yi a nan Amurka.
XS
SM
MD
LG