Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Asalin Somaliya Na Ficewa daga Kasar Yemen


'Yan asalin kasar Somaliya dake kokarin ficewa daga Yemen
'Yan asalin kasar Somaliya dake kokarin ficewa daga Yemen

Yakin dake gudana a kasar Yemen ya tislastawa 'yan asalin kasar Samaliya ficewa daga kasar suna komawa kasarsu

Majalisar Dinkin Duniya ta ce dubban ‘yan asalin Samaliya na komawa kasarsu daga Yemen inda yaki ya dai-daita, duk da cewa kasar tasu na fama da matsaloli iri-iri.

Ofishin Lura da Hakkin Bil Adama na Majalisar Dinkin Duniya yau Talata ya bayyana cewa a kalla mutane dubu 29 ne suka isa Samaliya daga Yemen tun watan Maris, mafi yawancin su mata da yara, kuma ana kyautata zaton za’a samu karin jama’a a watanni masu zuwa.

Wannan lamari shine sabanin abun da aka gani na tsawo shekaru masu yawa inda dubban daruruwan Samaliyawa suka bar kasarsu domin gujewa rigingimu, yunwa da talauci.

Kasar Yemen ta jure munanan rigigimu da aka share watanni ana yi, tsakanin ‘yan tawayen Houthi da dakarun dake goyon bayan shugaba Abdu Rabu Mansour Hadi.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG