Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Sun Bayyana Sunan Mahari Na Uku A Birnin London


Yau a Ingila, an tsaya tsit na minti daya a duk fadin kasar domin karrama wadanda harin ta'addanci da aka kai a birnin London ranar Asabar ya rutsa da su.

'Yan sandan Burtaniya sun bayyana sunan mahari na uku cikin maharan da jami'an tsaro suka kashe, sannan sun kama wani sabon mutum dangane da binciken da suke yi kan wannan hari.

Rundunar 'Yan Sandan birnin London ta hakikance cewa mahari na ukun da tun farko ba a bayyana kowanene shi ba, sunansa Youssef Zaghba, dan shekaru 22 da haihuwa.

Jami’an sun kara da cewa matashin dan kasar Italiya ne, amma asalinsa daga Morocco, wanda yake zaune a gabashin birnin London, kuma a baya babu wani abu gameda shi kan batun ta’addanci, Jiya ne hukumomin kasar suka bayyana sunayen mahara biyu.

Haka kuma 'yan sanda masu yaki da ta'addanci sun kama wani mutum dan shekaru 27 da haihuwa yau talata a yankin nan da ake kira Barking, amma basu ce komi ba kan dangantakarsa da harin da aka kai a karshen mako wanda ya hallaka mutane 7, da jikkata wasu 50.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG