Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A 'Yau aka daura auren Yarima William na Ingida da Catherine Middleton


Wannan hoton Yarima William ne da amaryarsa Gimbiya Kate, a lokacinda suke kallon shawagin jiragen saman mayakan saman Ingila a fadar Buckingham, bayan an daura musu aure.
Wannan hoton Yarima William ne da amaryarsa Gimbiya Kate, a lokacinda suke kallon shawagin jiragen saman mayakan saman Ingila a fadar Buckingham, bayan an daura musu aure.

A yauaka yi bikin daurin auren Yerima William da Catherine Middleton wadda yanzu itama ake kira Gimbiya Kate a wani kasaitatten biki a birnin London

Yau aka daura auren Yarima William da Catherine Middleton a wani kasaitattacen biki a Westminister Abbey a birnin London. Daga cikin wadanda suka halarci bikin daurin auren, harda tsohon Prime Ministan Ingila John Major. Ba'a dai gaiyace tsafin Prime Minista Tony Blair da Gordon Brown ba. An dai gaiyaci kimamin mutane dubu daya da dari tara, kuma an kiyasta cewa kimamin mutane miliyan biyu ne suka kali bikin ta akwatunan talibijin dinsu. Wannan biki shine mafi kayatarwa da Ingila ta gani, tun bikin iyayen Yarima William da aka yi tsakanin Yarima Charles da Gimbiya Diana a alif dari tara da tamanin da daya. Yan sanda dubu biyar aka girgirka a London domin nazarin dimbin mutane da suka taru a titunan birnin London domin suga ango da amarya. Shi dai Yarima William dan marigayiya Gimbiya Diana ne wadda tsohuwar matar Yarima Chales ne wadda ta rasu a sakamakon hatsarin mota a birnin Paris kasar Faransa kimamin shekaru goma sha hudu da suka shige. Ango da Amarya su baiyana jin dadin ga yadda jama'a suka jinjina musu tun a watan nuwamban bara lokacinda suka bada sanarwar cewa idan Allah ya yarda zasu yi aure. Yarima Willam jikan sarauniya Ingila Elizabeth ne.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG