Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Najeriya Zata Kara da Kasar Faransa a Gasar Cin Kofin Duniya


 Peter Odemwingie, daga tsakiya yake murnar culla kwallo a ragar kasar Bosnia.
Peter Odemwingie, daga tsakiya yake murnar culla kwallo a ragar kasar Bosnia.

A wasannin da aka yi ranar lahadi Netherlands ta doke Mexico, yayinda Costa Rica ta gama da Girka.

Yau litinin ake sa ran ci gaba da gasar cin kofin duniya a Brazil, inda Najeriya zata kara da kasar Faransa a zagayen “Nasara dole, ko kuma a tafi gida’. Za’a fara wasan ne da misalin karfe 4:30 zuwa biyar agogon Najeriya.

A wasannin da aka yi jiya lahadi, kasashen Costa Rica da Netherlands sun sami nasarar shiga zagayen quarter finals.

Costa Rica ta bada mamaki da ta sami hayewa daga rukunin farko tunda farko, sannan jiya ta gama da kasar Girka, bayan da aka yi bugun penalty, watau wasan daga kai sai mai tsaron gida, bayan da suka tashi da ci daya da daya. An kara musu lokaci, amma duk da haka aka tashi kunnen doki.

Tunda farko a jiya lahadi, kasar Netherlands ta baiwa Mexico mamaki bayan da ta doke kasar da ci biyu da daya.

XS
SM
MD
LG