Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Shugaba Buhari Zai Kaddamar Da Kamfanin Sarafa Sikari A Jihar Neja


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari
Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Yau shugaban Najeriya zai kaddamar da wani katafaren kamfanin sarafa sikari a jihar Neja wanda ya lakume kudi Nera miliyan dubu 50, zai ba mutane kimanin dubu 10 aiki da bunkasa noman rake a yakin da ma kewaye

Yau shugaban Najeriya Muhammad Buhari zai kaddamar da wani katafaren kamfanin sarafa sikari mai suna Sunti a garin Kusogi dake cikin karamar hukumar Mokwa a jihar Neja.

An kashe kimanin Nera miliyan dubu 50 wajen gina kamfanin kuma mutane sama da dubu 10 ne zasu samu aiki a kamfanin. Zai kuma bunkasa noman rake a yankin da kewaye.

Mataimakin gwamnan jihar Neja Alhaji Ahmad Muhammad Gyetso wanda shi ne shugaban kwamitin tarbar shugaban kasa, ya tabbatar da kammala duk wani shiri na karban Shugaba Buhari. Alhaji Gyetso ya kira hadin kan jama'a domin a gama bikin bude kamfanin lafiya.

Kazalika babbar jam'iyyar adawa, PDP ta bakin shugabanta na reshen jihar, Barrister Tanko Beji injishi, zuwan shugaban kasa jihar aleri ne garesu. Ya ce shugaban zai kaddamar da kamfanin da 'yan kasuwa masu zaman kansu suka gina abun da zai habaka tattalin arzikinsu. Ya yi fatan Allah ya kawo shugaban lafiya ya kuma mayar da shi gida lafiya.

Rundunar 'yan sandan jihar ta ce ta kara jami'an tsaro a wurin da za'a kaddamar da bikin.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:55 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG