Accessibility links

Kasar Najeriya na gudanar da mulkin demokradiyya a tafarkin federaliyya, wanda ya baiwa jihohi ‘yancin cin gashin kansu. Saboda haka abunda ke hada gwamnatin jihohi da na tarayya kalilan ne.

Amma zuwa Abuja domin taba alli da shugaban kasa ya zama tamkar kwalliya ga gwamnoni a Najeriya.

Masa na bayyana wannan lamari tamkar tafiya a tsarin mulkin soja.

Ko yaya al-umma ke kallon wannan lamari? Comrade Kabiru Sa’idu Dakata yace mafi yawan tafiye-tafiyen wadannan gwamnoni bashi da alaqa da aikin Jiha, face alaqarsu ta siyasa.

“Ba adalci bane ga talakawan da suka zabe su, kuma babbar inda illar take, bata lokaci da suke domin inda yana jihar shi, zai yi ayyukan da zasu taimaka wa Jihar. Abunda ake bata wa na biyu shine dukiyar al-umma.”

Mr. Dakata ya kara da cewa “kuma in ce kusan duka jihohin Najeriya suna da gidajensu mallakar jihar a Abuja. Gwamna yaje Abuja da shi da tawagarsa amma ka tsince su a otel”.

Ahmad Aruwa, wani jigo ne a jam’iyyar PDP ya bayyana haka a matsayin rashin madafa da gwamnonin Najeriya ke fama da shi.

“Gwamnonin suyi ta koke-koke suna cewa ai an bar musu gwamnati babu komai, kuma sun kasa zama su zauna su duba mene ne ya kamata su kirkiro a jihohinsu, da zasu samu cigaba ko su samu kudaden da zasu yiwa talakawan da suka zabe su aiki”.

Mr. Aruwa ya kara cewa “an debi motoci guda goma sha hudu, an zuba musu mai, amma duk daga karshe fa, sai su zo suna cewa a rage kudin ma’aikaci, a kori ma’aikaci, amma wadancan kudaden da ake kashewa motoci su ba matsala bane.”

Injiniya Bashir Yahaya Karaye cewa yayi wata kila gwamnatin da ta gabata ne ta sabawa wadannan gwamnoni yawan zuwa Abuja, amma hakan ba dai-dai ne ba.

“Tsarin mulki ya tsara komai yadda za’a tafiyar da aiki. Yace gwamna yayi aiki da ‘yan majalisar jiha. Gwamna ya nada kwamishinoni. Kowace ma’aikata ya nada kwamishina, saboda haka zuwa Abuja wani kawai da yake kaiwa fahimtar juna, ba ma demokradiyya ba, a tsarin aiki ma, bai dace ba.”

Ko yaya masana suke kallon wannan tafiye-tafiyen gwamnoni zuwa Abuja? Wani masanin ilimin demokradiyya Dr. Sa’idu Ahmad Dukawa yace alamun rauni ne yin haka.

“Bini-bini zasu tafi Abuja kamar suna mayar da mu tsarin da ake cewa ‘uniterism’ a turance, wato tsari irin wanda Ingila take kai.”

Masana sun bayyana yawan tafiye-tafiyen gwamnoni Abuja a matsayin rashin hikima da rashin sanin ma’anar ‘federaliyya’ da Najeriya ke yi.

XS
SM
MD
LG