Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za A Gufanar Da Mutanen Da Aka Taso Keyarsu Daga Birtaniya Gaban Kotun Amurka


Abu Hamza al-Masri,
Wadansu mutane biyar da ake kyautata zaton ‘yan ta’adda ne wadanda aka tura keyarsu a daren jiya daga Birtaniya da suka hada da limamin addinin Musulunci Abu Hamza al-Masri zasu bayyana a gaban kotunan Amurka cikin sa’oi 24.

Jiragen saman Amurka guda biyu sun iso Amurka yau da asuba, bayan tashinsu daga tashar jirgin mayakan saman Birtaniya ta British Royal jim kadan bayanda babbar kotun kasar ta ki amincewa da daukaka karar da Hamza da sauran mutanen suka yi.

Mutanen biyar sun gabatar da korafe-korafen da suka shafi harkokin shari’a da kuma hare hakin bil’adama da halin da suke gani zasu shiga a gidajen yarin Amurka. Da take fatali da daukaka karar, kotun Birtaniya ta bayyana cewa, tayi la’akari da abinda ya shafi al’umma.

Ana neman Hamza a Amurka ne sabili da laifuka da ake zarginsa da aikatawa da suka kunshi hada baki da kafa sansanin horas da ‘yan ta’adda a jihar Oregan. Ana kuma zarginsa da taimakawa wajen yin garkuwa da wadansu mutane goma sha shida da suka hada da Amurka biyu a Yemen cikin shekara ta dubu da dari tara da casa’in da takwas. Mutane hudu suka mutu sakamakon garkuwa da mutanen.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG