Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sakawa Wasu Jami'an Diflomasiyyar Pakistan Takunkumin Yawo a Amurka


Ofishin Jakadancin Pakistan A Washington DC
Ofishin Jakadancin Pakistan A Washington DC

Jakadan kasar Pakistan Aizaz Chudhary ya fadawa VOA cewa gwamnatin Amurka zata kakaba takunkumin hana tafiya kan wasu jami'an Pakistan wanda zai fara aiki a yau juma'a.

Ma'aikatar tsaron Amurka tace "Bata da wani abu da zata iya cewa akan lamarin a yanzu" amma a baya ta bayyana cewar tana da hurumin kakaba takunkumin tafiye tafiye karkashin dokar shirye shiryen kasashen ketare ta shekarar 1982.

A watan da ya gabata ne kafar yada labaran Pakistan ta bada rahoton cewa, za’a hana wasu jami’an diflomasiyya yawo ko kuma zuwa nesa da ofishin jakadancin Pakistan dake Washington DC da nisan kilomita 40 ba ta re da iziniba.

A baya dai jami’an diflomasiyyar Pakistan na da damar zuwa ko’ina a fadin Amurka ba tare da iyaka ba.

Ministan harkokin wajen Pakistan ya kira wannan lamari da kasashen biyu ka iya aiwatar dasu kan kowa, har da ma'aikatan diflomasiyyar Amurka, wasu lokutan suna fuskantar hani na tafiye tafiye a cikin Pakistan bisa dalilan tsaro.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG