Accessibility links

Zamu Hada Kai Da 'Yan Jarida Domin Inganta Tsaro - inji Sambo Dasuki


Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan

Mai ba shugaban kasar Najeriya shawara kan harkar tsaro Mohammad Sambo Dasuki yace ofishinsa zai hada kai da yan jarida domin inganta tsaro a kasar.

Yayi furucin ne a wani taron kara ma juna ilimi da ofishin nashi ya shirya domin wayar da kan mutane.

Taron ya samu halartar yan jaridu daga gidajen telibijan da rediyo da jaridu da mujallu, malaman addini da masana. An bada kasidu kan batutuwa daban-daban.

Dr. Fatima Akilu wata dirakta a ofishin Sambo Dasuki ta yi karin haske a kan taron. Tace idan ba an hada kai da yan jarida ba to ko za’a cigaba da fuskantar tashin hankali.

Tace su yan ta’ada sun san mahimmancin jarida don haka suna koyar da abun da Ku’arni bai koyar ba kuma mutane na yarda da abun da suka ce.

Ta dalilin haka Dr Fatima tace ya kamata ofishinsu ya soma anfani da yan jarida yana fitar da abun da Kur’ani ya koyas.

Kwararru a fannoni daban daban sun yi jawabi. Dr. Awal Anwar yace dole ne a koma ma tarihi a nemo mafita.

Yace a tsare gaskiya domin wanizibin idan nera ta gilma sai a yi watsi da gaskiya. Shi kuma Sheikh Mohammed Bn Usman limamin masallacin sahaba a Kundila Kano yace dole a kawar da bangaranci da rashin gaskiya da yin watsi da wasu kamar ba mutane ba ne a kuma koma ga Allah.

Jummai Yusuf daga Maiduguri wata yar jarida tace abun da gwamnati ta yi yanzu yana da kyau kuma tana fata abubuwan da suka fada a wurin taron za’a yi anfani da su.Daga karshe mahalarta taron sun gargadi ofishin mai ba shugaban kasa shawara a harkokin tsaro ya rika yin aikinsa a bayane ba tare da wata rufa-rufa ba.
XS
SM
MD
LG