Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zazzabin Masassara A Yankin Agadez Kasar Nijar Ya Hallaka Mutane Shida


Issoufou Mahamadou shugaban kasar Nijar

Barkewar zazzabin masassara a garin Zallet dake cikin jihar Agadez kasar Nijar ya yi sanadiyar mutuwar mutane shida amma tuni ma'aikatar kiwon lafiya ta kasa ta yiwa mutane gwaji inda ta gano wadanda suka kamu da cutar

Idrisa Maiga Muhammadou magatakarda a ofishin ministan kiwon lafiyar kasar Nijar shi ya bayyana barkewar zazzabin masassara da ta bulla agarin Zallet cikin jihar Agadez.

Sakataren ofishin ministan kiwon lafiya yace tun lokacin da suka samu labarin ne suka tura tawagar likitoci yankin domin yin binciken gaggawa. Cikin mutane hamsin da aka fara bincika, arba'in cikinsu na dauke da cutar.

Kawo yanzu dai mutane shida ne suka rigamu gidan gaskiya. Cigaba da binciken ya nuna mutane dari da biyu daga cikin mutane dari uku da goma sha uku da aka bincika suna dauke da cutar.

Wadanda suke fama da nunfashi likitoci sun ce hakan na faruwa ne sabili da tsananin sayin da ake fama dashi yanzu. Suna cigaba da wayewa al'umma kai dangane da irin matakan da ya kamata su dauka a wannan lokacin.

Duk marasa lafiyan an basu magani kyauta kana an sake bude wani asibiti wanda aka rufe watanni biyu da suka gabata yayinda mutanen China suka tashi.

Ga rahoton Haruna Mamman Bako da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:11 0:00

XS
SM
MD
LG