'Yan Sanda a Kenya Sun kashe Mutane Biyu Da Ake Zargi 'Yan al-Shabab Ne.

Bindigogi da albarusai da 'Yansanda suka gano a wani lamari na daban, har suka kama mutane biyu da ake zargi suna da alaka da al-Shabab.

Wadanda ake zargin kuma suna da alaka da kungiyar mayakan sakai ta al-Shabab dake Somaliya.

Sojojin Kenya da na Somaliya a garin Tabda, kasar Somaliya


Jiya lahadi,’Yan Sanda suka ce sun kai somamen ne da safiyar lahadi a wani gida dake wajajen fitar birnin Mombasa,a birnin ne babbar tashar jiragen ruwan kasar take.

Jami’ai suka ce an kashe daya daga cikin mutanen a cikin gidan, yayinda na biyun kuma, ya gamu da ajalinsa lokacinda yake kokarin gudu.

Wannan somamen shine na baya bayan nan, a fito na fito da ake tayi tsakanin ‘Yan Sanda, da masu kishin addini, da ‘yan aware dake kan gabar teku a kasar.

Magoya bayan al-Shabab sun sha kai hare hare domin nuna adawarsu da shawarar da Kenya ta yanke na tura sojoji zuwa Somalia, domin su yaki mayakan sakai masu zazzafar ra’ayi.