Duk da kokarin da hukumomi a Najeriya da Amurka ke yi na kame da kuma dakile ayyukan 'yan danfarar kudin Banki da aka fi sani da 419 ko yahoo Yahoo a Najeriya, har yanzu wasu 'yan Najeriya, musanman matasa, na ci gaba da gudanar da wannan muguwar sana'ar ta hanyoyi da dama.