Mutane sun yi dafifi a tsakiyar birnin Kano domin nuna fushinsu da janye rangwamin man fetir. Rahotanni na nuni da cewa, jami'an tsaro da kuma 'yan banga dake goyon bayan gwamnati sun kai hari kan masu zanga zangar lumana suka kashe a kalla mutane uku yayinda wadansu da dama suka ji raunuka.
Ga gargadi nan, wadan nan hotuna suna da muni ainun har suna iya tayar da hankali sosai, sabo da haka a yi hattara.
'Yan Najeriya dake zaune a Birtaniya sun yi dafifi a ofishin jakadancin Najeriya sake birnin London domin nuna rashin gamsuwa da tsare tsaren tattalin arziki masu tsauri da gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan ta dauka da suka kuntatawa 'yan Najeriya.
Wannan dandali ne dake nuna hotunan rayuwar yau da kullum ta mutane daga sassan duniya daban-daban. Sashen Hausa na Muryar Amurka yana baje muku su tareda fatar zaku kashe kwarkwatan ido da ganin canje canjen dake faruwa a ko wani mako a duniya.
Wasu sun kona tayu, wasu kuma suka rufe gidajen sayar da mai karfi da yaji a Lagos a ci gaba da tunzurin nuna kin jinin janye tallafi.
Kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin aikata wannan ta'asa.
Hotunan labaru mafi kai'ifarwa a 2011.
Domin Kari