Hukumar Kwallon Kafa Ta Duniya ko FIFA a takaice ta yi bikin sanarda jadawalin wasan cin kofin duniya na shekarar 2014 a garin Costa do Sauipe a Brazil ranar 6 ga watan Disambar 2013 Jadawalin ne ya bayyana kungiyoyin da zasu kara da juna a gasar kwallon kafa na bazara mai zuwa. Argentina da Najeriya suna rukuni daya na F kamar yadda aka hadasu a wasan da aka yi a Korea da Japan a shekarar 2002 da kuma Afirka Ta Kudu a shekarar 2010. Dama akan sa wadanda suka saba gasa da juna su biyu tare da sabbin zuwa biyu kamar Bosnia da Herzegovina da Iran
Shugaban Afirka Ta Kudu bakin fata na farko Nelson Mandela wanda ya yi fafaitikar yakar mulkin wariyar jinsi a kasar ya rasu yana da shekaru 95.
Okene yana aiki ne a matsayin mai dafa abinci cikin wani jirgin ruwa a gefen tekun Najeriya tun watan Yunin shekarar 2013. Yayin da wata muguwar guguwa ta taso kan teku sai jirginsu ya kife ya kuma nitse inda 'yanuwansa ma'aikata goma sha daya suka rasu amma shi Okene ya samu wani mafitar iska a jirgin wanda ya rike har ya yi kwana uku kafin wata kungiyar masu ceto daga Afirka Ta Kudu ta cetoshi.
Daruruwan wadanda ake zaton 'yan Boko Haram ne cikin motocin akorikura da motocin sojoji da suka sace suka yi anfani da su wurin kai hari kan sansanin mayakan sama a bayan garin Maiduguri da asubahin Litinin. Jami'ai da ganau sun ce mutane da yawa suka rasa rayukansu a harin da aka ce shi ne ya fi muni cikin 'yan kwanakinnan.
Dayansu zai shafe tsawon rayuwarsa a kurkuku a saboda samunsa da laifin shigar da makamai Najeriya, yayin da kwararru ke cewa wannan hukumci koma-baya ne ga hukumar 'yan sandan ciki ta DSS.
Rashin shugabancin na kwarai, da kin bin doka da oda da ‘yan kasa keyi, a mafi yawan sassan Jumhuriyar Afirka ta tsakiya ka iya jan hankulan kungiyoyin ‘yan ta’adda zuwa kasar daga sassa dabam-daban na Afrika.
Wani kakakin rundunar soja yace 'yan bindiga sun kai hare-hare kan kauyuka 4 yau talata da asuba a Jihar ta Filato
Domin Kari