An dai shafe kusan makwanni biyu da kafa dokar hana fitan tun daga maraice zuwa karfe shida na safe musamman a Jalingo fadar jihar Taraban.
Hukumomi a jihar Inugun Najeriya sun musanta rade-radin cewa an kori Fulani makiyaya daga garin Nenwe dake karamar hukumar Aninri na jihar, inda kuma hukumomin suka yi ittifakin cewa wannan mumunan sharri ne daga 'yan tada zaune tsaye.
Hare-haren biyu na zuwa ne kasa da makonni biyu da wnai harin Boko Haram da ya halaka mutum sama da 30 a wani gidan kallon kwallo a Maiduguri, sannan kasa da mako guda, bayan wani harin mayakan da halaka wasu dakarun Najeriyar.
Jiya a Kano aka bude wani taron koli na Jami’an sarrafa kudade a ma’aikatu da hukumomin gwamnatocin tarayya da na jahohi a Najeriya, wanda ofishin babban Akanta Janar na kasar ya shirya kan dabarun alkinta dukiyar kasa.
Domin Kari