Jamiāan kasar Afghanistan sun ce wasu tagwayen harin kunar bakin wake a Kabul, babban birni kasar ya kashe akalla mutane 22, wasu su 70 kuma sun jikkata.
Jami'ai a Koriya ta Kudu, sun ce sun hakikance barazanar da Koriya ta Arewa tayi a baya bayan nan cewa, zata harba makami mai linzami mai cin dogon zango,tayi ne da nufin tsara wata dangantaka da sabuwar gwamnatin Amurka ta Donald Trump.
Amurka ta kama ta kuma tuhumi wani tsohon babban jami'in kamfanin kera motoci ta Volkswagen a Amurka kan zargin hada baki da niyyar zambar Amurka kan magudin irin hayaki da motocin kamfanin suke fitarwa.
Fadar shugaban Rasha ta Kremlin tana Allah wadai da cewa zargin da hukumomin leken asirin Amurka suke yiwa kasar cewa tayi shishshigi cikin harkokin zaben Amurka da zummar taimakawa Donald Trump, a zaman wanda bashi da tushe kuma tamkar wasan yara ne ko rashin kwarewa.
Har yanzu Amurka da kawayenta na cigaba da kai farmaki akan sansanonin kungiyar ISIS dake cikin kasar Syria da Iraq
Yau Talata majalisar dattijai zata fara tantance wasu daga cikin mutanen da shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump ya zaba domin basu mukaman ministoci karkashin gwamnatinsa.
Yayin da 'yan jam'iyyar Republican, ciki har da Shugaba mai jiran gado Donald Trump, ke dada kusantar gwamnatin Taiwan, kasar China ta bayyana damuwarta
Mutumin nan da ya kai hari a wani filin jirgin sama a Florida ya gurfana gaban kotu. Cikin tuhumce-tuhumcen da ake masa har da na kashe mutane biyar da kuma raunata wasu.
A yayinda hukumar leken asirin Amirka ta tantance cewa kasar Rasha tayi shishigi a zaben shugaban Amirka, shugaba Barack Obama yace yayi kuskuren hasashen irin tasirin da yakin neman zaben karya da satar shiga computa zai dora akan tsarin mulkin demokradiya.
Gidan talibijin na kasar Iran ya bada sanarwar rasuwar tsohon shugaban kasar, jagaban sauyi Akbar Hashemi Rafsanjani.
Fadar White House ce ta ada wannan umarni ranar Jumma'a.
Hakan yana kunshe cikin wani rahoton sirri da aka bayyana ranar Jumma'a.
Domin Kari