A yau Litinin kungiyar IS ta dauki alhakin harin da aka kai a ranar da sabuwar shekara ta kama a wani gidan rawa a birnin Istanbul dake Turkiyya.
Jami’an Amirka sun ce basu da bayanin cewa anyi satar shiga kamfanin bada wutar lantarki a jihar Vermont dake arewa maso gabashin Amirka, a yayinda suke ci gaba da binciken wata na’urar satar bayanai da aka samu cikin injin mai kwakwalwa irin wanda ake rikewa.
Sa’a guda kafin a shiga sabuwar shekara kasar Turkiya ta fara kirga gawarwarkin mutane da aka kashe a wata mashaya a gabar tekun birnin Istanbul.
Yau Lahadi Mr. Guterres na Portugal ya kama aiki, bayan da wa'adin Mr. Ban ya kare a daren jiya Asabar.
Kasashen New Zealand, da Australia da Rasha suna jerin kasashen da suka fara ganin sabuwar shekara.
Tattalin arzikin kasar Philippine ya habbaka fiye da duk wata kasar kudu maso gabashin Asia a wannan shekarar, sakamakon huldar diplomasiya da China, Japan da kuma karuwar kashe kudade a fannin gine-gine.
Kasar Rasha tace ba zata 'dauki matakin korar jami'an diflomasiyyar Amurka ba, a matsayin mayar da martani ga takunkumin da Amurka ta kakaba mata.
Gwamnatin Amurka ta kakabawa kasar Rasha wani sabbin takunkunmi a matsayin martini kan shisshigi da kuma satar bayanan da ake zargin Rasha ta yi a zaben shugaban kasar Amurka da aka yi a watan Nuwamba.
Domin Kari