Hukumomin Australia sun fara tuhumar wani matashi da ake zargi da yunkurin kai hari akan dandazon jama'a a lokacin bukuwan sabuwar shekara.
Hukumar da ke yaki da cuta mai karya garkuwar jikin dan'adam a kakashin Majalisar Dinkin Duniya, ta ce ana kara samun hanyoyin kai wa ga magunguna.
Zanga zangar da kungiyoyin addinin Islam suka yi ta koma tarzoma a ranar Asabar yayin da ‘yan sanda suka yi kokarin tarwatsa tarin zanga zangar, inda jami’an tsaro 100 da masu bore dama suka ji raunuka.
Duk da tashin bam a masallacin 'yan darikar Sufi da ya hallaka daruruwan jama'a da raunata wasu da dama, mabiya darikar sun ce suna ci gaba da gudanar da shirye shirye.
A wani yunkuri na dai-daita al'amura da jan hankalin kasashen duniya akan yanayi da matsalolin da suka addabi 'yan kabilar Rohingya a kasar Myanmar, shugaban cocin Katolika Paparoma Francis na ci gaba da ziyara a kasar.
Yau lahadi 'yan kasar Nepal ke jefa kuria, a zaben farko da ake gudanarwa a kasar, kuma an tsara zaben gida biyu ne, wanda ake fatar ganin jamaa masu jefa kuria sun fito kwansu da kwarkwatar su.
An gudanar da zanga-zangar lumana a kaashen yammacin Turai domin karrama ranar kare mata a duniya,inda da farko an samu tirjiya a kasar Turkiyya kafimn muhunta su sa baki.
Jiya Asabar dubban mutane ne a kasashen Turai su ka fito zanga-zanga domin karrama ranar kawar da cin zarafi ga mata ta duniya.
Domin Kari