Ahalinda ake ciki kuma,kimanin manyan jami'an difilomasiyya da wasu ma'aikata- a ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka su kusan dubu daya sun rattaba hanu kan takardar koke ko nuna rashin amincewa kan sabon dokar da shugaba Trump ya bayar na hana wasu mutane daga kasashen musulmi 7, yin balaguro zuwa Amurka. Jiya Talata ahukumance aka mika wasikar.