Babbar Kungiyar bunkasa harakokin ciniki ta kasashen nahiyar Latin Amurka ta Mercosur ta dakatar da wakilcin kasar Venezuela a kungiyar, a sanadin matakin da sabuwar majalisar yi wa kundin tsarin mulki ta Venezuela ta dauka na sallamar babbar lauyar gabatar da shara’oi ta kasar, Luisa Ortega.