Shugaba Donald Trump ya zairgi 'yan Jarida da kin yada kalaman da yayi na cewa, "nuna wariyar launin fata mummnan abune".
Karshenta dai 'yan sandan Spain sun harbe mutumin da ake zaton shine direban motar nan da akayi anfani da ita wajen kai harin ranar Alhamis da ya hallaka mutane a Barcelona har lahira.
'Yan kasar Hong KOng sunyi bore akan hukuncin da gwamnatin kasar ta yanke aka wasu mutane 3 masu rajin kare demokaradiyya.An yanke musu hukunci dauri ko biyo bayan rawart da suka taka na nuna kyamar gwamnati tun a shekarar 2014
Kasar Iraq ta kaddamar da wani farmaki yau Lahadi da safe da nufin sake kwace Tal Afar, wani gari dake gabashin Mosul, daga hannun mayakan IS.
Majalisar dokokin kasar Venezuela da ‘yan adawa ke jagoranta, ta yi wani zama a jiya Asabar, inda ta yi watsi da karfin ikon da sabuwar majalisar dokokin kasar ta baiwa kanta na yin doka.
Mai yiwa ne an kashe direban da motar da ya kai hari ya kashe mutane a birnin Barcelona ranar Alhamis.
Hukumomin kasar Spain ko kuma Andalus, sun bayyana cewa sun kashe madugun da ya jagoranci harin motar da ya kai ga mutuwar mutane sama da goma a kasar a ranar Alhamis.
Fara Ministan Spain ya ayyana kwanaki uku domin zaman makoki da jimamin mutanen da suka rasa rayukansu a harin da aka kai da mota ranar Alhamis.
Trump yayi sabon furucin ne a zauren ofishinsa dake birnin New York jiya Talata, inda ya yi jawabi akan sake gina kayayyakin more rayuwa a Amurka.
Wasu daga cikin shugabannin kasashen yankin Latin Amurka, sun fara maida martani kan barazanar matakin soji da shugaban Amurka Donald trump ya ce zai dauka a kasar Venezuela domin dawo da tsarin mulkin dimokaradiyya.
Ambaliya ruwa sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya ta yi sanadin rayukan mutane sama da 30 a kasar Nepal.
Tuni aka umarci sojoji da 'Yansanda da farar hula su fara aikin ceto wadnda suka makale kan gine gine
Domin Kari