A wani yunkuri na kara farfado da harkokin kasuwanci da tattalin arziki, kungiyar tarayyar Turai da kasar Japan sun rattaba hannu akan wata yarjejeniyar cinikayya.
Manyan kungiyoyin leken asirin Amurka da kasashen tarayyar Turai sun nuna kaduwa da kushe kalaman shugaba Trump, akan hakikance cewa kasa Rasha bata yi wa zaben Amurka katsalanda ba.
Gabanin taron, shugaba Donald Trump ya ce dangantakar dake tsakanin Amurka da Rasha ta fuskanci koma baya a cikin shekarun da suka gabata.
Amurka ta ce tana shirin sake sanya takunkumi karya tattalin arziki akan Iran a farkon watan Agusta.
Manyan jami’an Amurka da na Afghanistan da yawa sun tabbatar da wannan matakin, a cewar jaridar.
Shugaban Amurka Donald Trump ya shawarci Firai Ministar kasar Birtaniya Theresa May ta kai karar Kungiyar Tarayyar Turai turai maimakon tattaunawa da kungiyar, a shirin ficewar kasar daga kungiyar.
Yayin da zargin katsalandan din Rasha a zaben Amurka ke kara janyo takaddamar siyasa a cikin Amurkar, Shugaban Amurka Donald Trump ya sha alwashin tinkarar Shugaban Rasha muddun su ka yi tozali a Helsinki.
Bayan da kafafen yada labaran Burtaniya su ka yi ta yada labarin da ya samo asali daga jaridar The Sun ta Burtaniyar, cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya caccaki Firaminista Theresa May
Wani farmaki ta sama ya kashe akalla mutane 54 ciki har da mayakan IS da kuma fararen hula 28 a gundumar gabashin Syria ta Deir Ezzor a cewar masu sa ido a kan take hakin bil adama.
Ana zargin 'yan sandan Pakistan sun yi awon gaba da wasu magoya bayan tsohon firai ministan kasar Nawaz Shariff kwana guda kafin ya koma kasar tare da yarsa Maryam Shariff wadda ake kyautata zaton zata gajeshi asiyasance
Kamar yadda mazauna birnin London suka sha alwashi da isar shugaban Amurka jama'ar garin suka fantsama cikin zanga zangar kin jinin shugaban Amurka Donald Trump
Wani babban hafsan sojan Isra’ila yace hare-haren da jiragen saman kasarsa suke kai wa a Syria sun takura yunkurin da Iran ke yi na samun mazauni a kasar
Domin Kari