Sakamakon wani bincike da aka fitar, ya nuna cewar Korea ta Arewa da Eritrea, sune kasashen da aka fi samun matsalolin aikin bauta a duk fadin Duniya.
Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan tawayen kasar Syria sun cimma yarjejeniyar ajiye makaman su a kudu maso yammacin wuraren dake kusa da yankin Golan, wanda Isra’ila ta mamaye.
An janye dokar ta-bacin da aka sanya a kasar Turkiyya biyo bayan yunkurin yiwa shugaba Rajib Tayip Erduwan, juyin mulki da bai samu nasara ba a shekarar 2016.
Mako guda bayan da aka ceto su daga wani kogo da suka makalle a cikinsa, yanzu haka matasan ‘yan kwallon kafar nan na kasar Thailand da kocin su na kan hanyarsu na komawa gidajensu don sake hadewa da iyalan su.
A wani yunkuri na kara farfado da harkokin kasuwanci da tattalin arziki, kungiyar tarayyar Turai da kasar Japan sun rattaba hannu akan wata yarjejeniyar cinikayya.
Manyan kungiyoyin leken asirin Amurka da kasashen tarayyar Turai sun nuna kaduwa da kushe kalaman shugaba Trump, akan hakikance cewa kasa Rasha bata yi wa zaben Amurka katsalanda ba.
Gabanin taron, shugaba Donald Trump ya ce dangantakar dake tsakanin Amurka da Rasha ta fuskanci koma baya a cikin shekarun da suka gabata.
Amurka ta ce tana shirin sake sanya takunkumi karya tattalin arziki akan Iran a farkon watan Agusta.
Manyan jami’an Amurka da na Afghanistan da yawa sun tabbatar da wannan matakin, a cewar jaridar.
Domin Kari