An dakatar da jigilar mutane a wasu tashoshin, wanda hakan yasa mutane bin dogon layi don shiga motocin bas kyauta, don isa wasu tashoshin jirgin.
Shugaban gidan yarin jihar, Jarbas Vasconcelos, ya fada a cikin wata sanarwa cewa ‘yan wata kungiyar fursuna, mai suna Comando Classe A, ne suka saka wuta a dakunan kwanan abokan hamayyarsu na kungiyar Comando Vermelho.
An kashe wasu sojojin Amurka biyu a bakin daga, a wani al'amarin da ake ganin irin harin nan ne na sojoji masu canza sheka.
Mousavi ya fadawa taron manema labarai da aka yada shi kai-tsaye a gidan talabijin na Press TV cewa, tattaunawar da kuma zaman sulhun zai yi wu ne idan aka tsara batutuwan da za a tattauna akai a kuma samu sakamakon mai kyau.
An samu tankiya a daren jiya Lahadi a Hong Kong ya yin da masu zanga zanga ke kara bazuwa a kan titunan birnin, kana suna bijirewa ‘yan sanda da suke jefa musu barkonon tsohuwa da albarusan roba a cikin sa’o’I da dama.
Sabon tsokaci daga Pyongyang ya kara jefa shakku kan tattaunawar makaman nukiliya
Johnson ya yi alkawarin hada kan al’ummar kasar yayin da ya ke murnar sakamakon kuri’ar da aka kada na Jam'iyyar Conservative.
Domin Kari