Ranar Litinin aka fitar da wani faifai da kuma hotu da aka hakikanta cewa Leah Sharibu ce, daliba daya tilo da kungiyar Boko Haram take rike da ita daga cikin daliban makarantar sakandaren Dapchi dari da goma da ta sace ranar goma sha tara ga watan Fabrairu, da ta saki ranar shirin da bakwai ga watan Maris na wannan shekarar.