Ziyarar ta shugaban na zuwa ne a daidai lokacin da aka dakatar da wasu ayyukan gwamnati tsawon kwanaki 19, a yayinda shugaba Trump ke neman kudin gina katanga a bakin iyakar kasar da Mexico.
Mai bincike na musamman kan shishigin Rasah akan zaben Amurka, yace shugaban kamfe Paul Manafort yayi mishi karya.
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ce ana ci gaba da samun karuwar matsalolin jin kai da na tsaro a iyakar da ke kudancin kasar, ya na mai kiranta a matsayin matsala mai sosa zuciya.
A yau Talata ake sa ran shugaba Trump zai yi wani jawabi ta talabijin ga al’umar kasar, gabanin ziyarar da zai kai kan iyakar ta Amurka a ranar Alhamis.
Shugaban Amurka Donald Trump yace zai yiwa kasar jawabi a yau Talata kan abin da ya kira “matsalolin jinkai da tsaron kasa” dangane da kan iyakar Amurka da kasar Mexico, kafin ya je wurin a ranar Alhamis, saboda ya gane ma idonsa irin kokarin da ake yi na hana kwararowar bakin haure cikin Amurka.
Ma’aikatan majalisun tarayyar Amurka da jami’an fadar White House sun gana a jiya Asabar a nan Washington, a wani kokarin kawo karshen rufe wani bangaren gwamnati da ya shiga kwana na cikon 15, kuma an kammala wannan tattaunawa bayan wasu sa’o’i. Bangarorin biyu na kuma shirin ganawa a yau Lahadi.
Da alamar batun rufe wani bangaren gwamnatin Amurka ba zai kare nan da nan ba, yayin da hadiman fadar White House da na majalisun tarayya zasu yi ganawa a karshen mako.
Ma'aikatar Harkokin Waje ta Mexico ta bukaci Amurka a hukumance da ta yi cikakken bincike akan harba barkonon tsohuwa da jami’an tsaron Amurka sukayi a bakin iyakar Mexico.
Shugaban Amurka na neman maslaha da 'yan majalisun kasar, don kawo karshen rufe wasu ma'aikatun gwamnati.
Shugaban Amurka Donald Trump yana neman hanyar kawo karshen rufe wadansu ma'aikatun gwamnati duk da yake har yanzu dukan bangarorin sun ja daga kan matsayarsu.
“Amma idan Amurka ta kai mu makura, har ta tilasta wani abu akanmu, ta hanyar kakaba takunkumi ba tare da cika alkawuran da ta dauka a gaban duniya ba, ba mu da wani zabi, da ya wuce mu dauki wata sabuwar hanya.” In ji shugaba Ki
Yayin da aka yi ban kwana da shekarar 2018 aka kuma shiga ta 2019, wasu kwararru na ganin an samu cigaba da kuma cibaya a 2018. Kuma shekarar 2019 za ta gaji wasu al'amura na 2019 na alheri da kuma matsala.
Domin Kari