Masu hasashen yanayi a Amurka suna jan hankalin jama’a dangane da matsalolin ambaliyar ruwa da za’a iya samu a tsakiyar kasar yau Talata.
An jadadda muhimmancin Karfafa dangantakar soji tsakanin Amurka da Japan, ganin irin yadda China ke ta kara zabura.
Yayin da shugaba Donald Trump ke ziyara a Japan, mataimakinsa Mike Pence, ne ya ajiye furanni a gaban kabarin wani soja da ba’a san sunansa ba a makabartar da ke Arlington
Kalaman shugaban Amurka Donald Trump da mai bashi sahawara a kan tsaron kasa John Bolton a kan barazanar shirin makaman nukiliyar kasar Korea ta Arewa sun bambanta da juna.
A wata zaman da aka saba yi a dakin Roosevelt a fadar White house a jiya Alahamis, a kan sanar da tallafin kudi dalar Amurka biliyan sha shidda ($16b) ga manoma, ya rikide ya koma zaman cin mutuncin tawagar manyan ‘yan Democrats a majalisar tarayya da shugaban kasa ya musu.
Sakataren tsaro mai rikon kwarya Patrick Shanahan, ya karyata rahotanni dake cewa za a aika dakarun Amurka dubu biyar zuwa dubu goma zuwa yanki Gabas ta Tsakiya domin dakile barazanar da Iran ke yi.
Daga cikin jami’an, har da Sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo, mukaddashin Sakataren tsraon Amurka, Patrick Shanahan da kuma shugaban hafsan hafsoshin dakarun kasar Janar Joseph Dunford.
Fadar White House ta umarci tsohon Lauyarta kada ya bayyana a gaban Majalisar tarayya, kamar yadda ma’aikata Shari’a ta shawarta.
Domin Kari