Dan shekaru 66 da haihuwa Epstein yana fuskantar shari’a kan tuhume tuhuman gwamnatin tarayya na safarar mata da ake lalata da su da ya hada da yara mata kanana da wasunsu shekarun su bai gaza goma 14.
Amurka ta jinkirta sabon harajin kashi 10 cikin 100 akan wasu kayayyaki da China ke shigarwa kasarta, wanda ya kamata ya fara aiki ranar ‘daya ga watan Satumba.
An kammala zaman da aka kwashe kwanaki 9 ana yin sa a Qatar da goshin Asuba a yau Litinin, a cewar wani dan kungiyar ta Taliban.
A ranar Litinin din da ta gabata, Amurka da Korea ta Kudu suka fara atisayen, wanda ake shirin kammala shi a ranar 20 ga watan nan na Agusta.
Jiya Alhamis, magadan gari sama da 200 a Amurka, sun bukaci ‘yan majalisar dattawa da su dawo daga hutun lokacin barazar "Summer", su rattaba hannu kan kudurin dokar dakile wanzuwar bindigogi.
Shugaban Donald Trump ya kai ziyara tare da mai dakinsa, don jinjinawa wadanda suka fara kai daukin farko da kuma tattunawa tare da iyalai da suke zaman makoki da wadanda suka tsira daga wannan bala’in.
Ofishin babban hafsan sojan Koera ta Kudu ya ce Korea ta Arewa tas Arewa sake ta cilla wadanan makaman masu linzami masu cin matsakaicin zango guda biyu, zuwa yammacin kasar ne.
Da ya ke mai da martani kan hare-haren kan mai uwa da wabin nan da aka kai a Amurka, Shugaban Amurkar Donald Trump ya sha alwashin, abin da ya kira, daukar matakin gaggawa.
Donald Trump ya bukaci a sauke tutocin kasar a gine-ginan gwamnati har na tsawon kwanaki biyar masu zuwa yayin nuna alhini.
A wani zub da jini na tsawon sa’o’I 13 a Amurka, wasu mahara biyu a wurare daban daban, sun kashe mutane 29 kana suka jikata wasu da dama, yayin da hukumomi ke binciken musabbabin wadannan munanan hare hare.
Domin Kari