Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Bullo Da Hanyar Kare Makarantu Daga Ayyukan 'Yan Ta'adda


Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani
Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani

Gwamnatin jihar Kaduna ta fito da wani tsari na hada makarantu 359 wuri daya saboda karuwan ayyukan ‘yan fashin daji lamarin da yasa aka samu yawan sace mutane da yin garkuwa dasu a jihar.

Da yake jawabi a wani taron masu ruwa da tsaki na horar da wata rundunar kare makarantu a ranar Laraba, a ta bakin mai wakiltan Gwamna Uba Sani, babban jami’in oshifin gwamna Sani Kila, ya ce makarantun dake uguwanni da basu da kariya, za a tattar su wuri daya mai cikakken tsaro, a wani matakin kare makarantu da ‘yan makaranta daga harin barayin dajin.

A cewarsa, an kaddamar da wannan rukunin masu bada kariya ga makarantu a karkashin shirin gwamnatin tarayya na tsare lafiyar makarantu ne da zummar kare makarantun da yara da kuma malaman su daga duk wani nau’i na harin barayin daji da ‘yan ta’adda.

Yayin da yake bayyana cewa jihar Kaduna na daya daga cikin jihohin da ke yaki da ‘yan fashi da ta’addanci da garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka, Kila ya koka da yadda ayyukan wasu da ba jami’an gwamnati ba ke kawo cikas ga harkokin zamantakewa da tattalin arziki a cikin al’ummar da lamarin ya shafa kana suna barazana ga shirin farfado da ilimi a jihar.

“Tsarin ilimin jihar Kaduna na fuskantar matsalar raguwar shiga makarantun, inda aka samu adadin daliban firamare da za su shiga makaranta ya gaza da 200,000 a shekarar karatu ta 2022/2023 idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata. Wannan gagarumin raguwa (daga 2,111,969 a shekarar 2021/2022 zuwa 1,734,704 a cikin 2022/2023) an danganta shi da yawa da rashin tsaron makarantu," in ji Kila.

Jihar Kaduna kamar sauran jihohin Arewa Maso Yamma, ta sha fama da matsalolin tsaro masu tsanani da ‘yan fashin daji da ‘yan ta’adda suka haddasa, ciki har da hare-hare kan makarantu.

Sai dai Kila ya ce ya yi imanin cewa, babu wata kasa da za ta iya cimma burinta na raya albarkatun jama’a, kuma ta ci gaba da bin tafarkin samun ci gaba mai dorewa a lokacin da makarantunta ke fuskantar barazanar rashin tsaro.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG