Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Vinicius Zai Tafi Jinyar Wata Biyu


Vinicius Junior a lokacin da ya ji raunin a wasan Brazil da Colombia
Vinicius Junior a lokacin da ya ji raunin a wasan Brazil da Colombia

Kungiyar ta Madrid ba ta ba da takamaiman lokacin da Vinicius zai kwashe yana jinya ba, amma irin wannan raunin kan dauki dan wasa watanni biyu kafin ya warke.

Dan wasan Real Madrid Vinicius Junior ya ji rauni a kafarsa ta hagu yayin da Brazil ke karawa da Colombia a wasan neman gurbin shiga gasar kofin duniya.

Vinicius ya ji raunin ne a ranar Juma’a inda Colombian ta lallasa Brazil da ci 2-1.

Hakan ya sa dole aka canja shi a wasan tun kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Kungiyarsa ta Madrid ta ce gwajin da aka masa a ranar Asabar ya nuna cewa Vinicius ya yada jijiyarsa ne.

Kungiyar ta Madrid ba ta ba da takamaiman lokacin da Vinicius zai kwashe yana jinya ba, amma irin wannan raunin kan dauki dan wasa watanni biyu kafin ya warke.

Madrid dai t riga ta kai matakin kwaf daya a gasar Zakarun Nahiyar Turai.

Akwai tazarar maki biyu tsakaninta da Girona mai jan teburin gasar ta La Liga bayan zagaye 13 da aka yi a gasar ta Sifaniya.

Dandalin Mu Tattauna

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG