No media source currently available
Wata fashewa a wani masallaci dake kauyen gadan, na karamar hukumar gezawa ta jihar kano ya raunata kimanin mutane 27. Al’amarin ya faru ne da misalin karfe 5 da mintuna 20 na safiya yayin sallar asubahi.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya EFCC ta ce kashi saba’in cikin dari na matsalar zarmiyar kudi da almundahana a kasar, a bangaren hada-hadar banki ake aikata su. A kowacce shekara, dubban ‘yan Najeriya su na kai rahoton almundahana ga hukumomi.
Shirin Taskar VOA na wannan makon ya duba al’amuran cin hanci da rashawa ne a kasashen Afirka. A farkon wannan shekarar, Transparency International, cikin rahotonta na 2023, ta ce yaki da cin hanci da rashawa ya fuskanci koma-baya sosai, inda a wasu kasashen, babu abunda da aka cimma a game da haka.
Shirin Lafiyarmu na wannan makon ya yi nazari ne akan dawainiyar haihuwa da rainon yara da iyaye mata ke yi – wani babban aiki mai faranta rai da kuma yake tattare da kalubale ga lafiyar kwakwalwarsu.
Hakuri tsakanin matasa ya kan zamo abu mai matukar wuya, ta yaya matasa zasu rungumi akidar hakuri da juna, da abin da rayuwa ta zo da shi?