Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Rufe Tafsirin Ramadan Na Bana A Masallatan Abuja


Musulmai a Najeriya da ma wasu sassa a duniya suna azumi a wannan wata mai tsarki na Ramadan da kama baki daga daren assubahi zuwa magariba.
Musulmai a Najeriya da ma wasu sassa a duniya suna azumi a wannan wata mai tsarki na Ramadan da kama baki daga daren assubahi zuwa magariba.

Manyan malamai sun yi kira ga al'umma da su ci gaba da sadaukar da kawunansu ga bautar Allah da taimakawa juna ko bayan Ramadan

Manyan malaman addinin Islama dake yin tafsiri a duk watan Ramadan, sun fara rufe tafsirin na bana a saboda gabatowar karamar Sallah ta Eid el-Fitr.

An fara gudanar da irin wannan karatu na Tafsir, inda ake koyarda ma'anonin kalmomin al-Qur'ani Mai Tsarki tun farkon watan Azumin ramadan.

Sheikh Nasiru Abdul-Muhyi na masallacin Maitama, yace irin wannan tafsiri na watan Ramadan yana da fa'ida da kuma lada mai yawa, ga wanda yake ji, da wanda yake karanta Ayoyin da kuma mai fassarawa.

Sheikh Abdullahi Bala Lau dake rangadin majalisun tafsiri na kungiyar Izala yace alamun an karbi ibada da addu'o'in mai azumi sune a ga mutum ya zamo mutumin kirki a bayan Ramadan a saboda ya karu da karantarwar da ya samu cikin watan.

Ga cikakken rahoton da Nasiru Adamu el-Hikaya ya aiko daga Abuja...
An Kawo Karshen Tafsiri Na Bana A Masallatan Dake Abuja - 1:53
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:53 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG