Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Sora' Yayi Sanadin Dakatar Da Shirin Fadada Dakin Harhada Fina-Finan Tyler Perry


OpenAI-Sora Explainer
OpenAI-Sora Explainer

Hakan ya biyo bayan da ya kalli bajintar da mutum-mutumin Sora, me amfani da kirkirarriyar basirar wato AI yayi, wacce ta bada damar mayar da rubutaccen labarin dake kan na’ura zuwa bidiyo.

Fitaccen mai shirya fina-finan nan Tyler Perry ya dakatar da shirinsa na kashe dala milyan 800 wajen fadada wurin harhada fina-finansa dake jihar Atlanta Georgia.

Tyler Perry ya shaidawa dan jaridar dake daukar rahotannin masana’antar shirya fina-finan Hollywood cewar, mutum-mutumin Sora da aka fara amfani dashi a ranar 15 ga watan Fabrairun da muke ciki zai iya aikata wadannan al’amura wani abu ne daban, amma ganin zahirin bajintar daya aikata ta tafi da tunanina.”

Perry, wadda Netflix ya fara haska wani fim dinsa mai suna, “Mea Culpa” a Juma’ar data gabata, yace aikin fadada wurin harhada fina-finan na iya samar da karin matakan fidda sauti guda 12.

"Saidai yanzu dukkanin wannan ya tsaya chak,” shawarar kenan da Perry ya yanke a matsayin martani ga irin tasirin da basirar mutum-mutumin Sora za ta iya yi akan harkar shirya fina-finan a yadda take a halin yanzu.

Perry, na hangen wani yanayi da zai sanya shirin daukar fim a dandali ko wani gini ya zamo tarihi.

A cewar Perry, mun sha tattaunawa akan batun a shekarar data gabata, cewar al’marin nan na zuwa, saidai ban fahimta ba har sai dana kalli gwajin irin bajintar da zata iya samarwa. al’amarin yayi matukar ban mamaki.”

Dandalin Mu Tattauna

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG