Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Ya Ce Zaben Ranar Alhamis A Kasar Iraqi Shine Harsashin Dimokuradiyya A Tsakiyar Gabas Ta Tsakiya


Shugaba Bush ya ce zaben da aka gudanar ranar alhamis a kasar Iraqi yana cike da tarihi, ya kuma karfafa kawa a yaki da ta'addanci. Sai dai kuma a cikin jawabin da yayi ga Amurkawa, ya yi kashedi game da gaggawar janyewa, yana mai fadin cewa yin hakan zai haddasa mummunar illa.

Wannan shine jawabin farko da shugaba Bush ya gabatar daga ofishin shugaba, ko Oval Office, tun lokacin da ya bayar da sanarwar kai farmaki kan kasar Iraqi a watan Maris na 2003. Mr. Bush ya ce har yau, akwai Amurkawa da dama dake tababar yawan kudin da ake kashewa da kuma inda yakin Iraqi ya dosa. Ya ce akwai sabanin ra’ayi game da manufofinsa kan Iraqi, amma kuma ya kara da cewa ya kamata bukatar tabbatar da nasara ta zamo mafi a’ala a zukatan kowa.

Shugaba Bush ya yarda cewa za a samu karin zub da jini da sadaukar da rai nan gaba, amma kuma ya ce tabbatar da ’yancin Iraqi ya cancanci wannan sadaukar da kai. Ya ce a wasu lokuta ba a iya ganin irin ci gaban da ake samu a saboda irin tashin hankalin dake faruwa, amma kuma ana samun ci gaba kamar zaben ranar alhamis, inda dimokuradiyya ta kafu da gindinta a tsakiyar gabas ta tsakiya.

Shugaban an Amurka ya kara da cewa, "Ga kowace barna guda a kasar Iraqi, akwai ci gaba mai yawa da aka samu wajen sake gina kasa da karfafa fata. ga kowane rai da aka yi hasara, akwai rayuka da dama da aka ceto. Kuma ga kowane dan ta’adda dake neman hana kafa ’yanci a Iraqi, akwai ’yan Iraqi da Amurkawa da yawa dake kokarin murkushe su. ’Yan’uwana Amurkawa, ba wai zamu iya samun nasarar yakin Iraqi ba ne, muna samun nasarar a yanzu haka."

Shugaba Bush ya fito balau balau yana sukar masu sukar manufarsa kan iraqi da kuma kiran da suke yi na a gaggauta janye sojojin Amurka. Ya ce yana da muhimmanci a fahimci irin mummunar illar da zata biyo bayan janyewa kafin Amyrka ta kammala aikin da ya kai ta can. Ya ce, "Idan muka janye cikin gaggawa, zamu watsar da abokanmu ’yan Iraqi, zamu kuma nunawa duniya cewar Amurka ba abar yarda ba ce domin ba ta cika alkawuranta."

Wannan jawabin na shugaba Bush ya gabatar da shine a wani bangare na matakan da gwamnatinsa ke dauka domin lallashin Amurkawa su yi na’am da manufofinsa kan Iraqi a daidai lokacin da kuri’un neman ra’ayoyin jama’a ke nuna cewa karin jama’a suna komowa daga rakiyar wannan yaki. Masu sukar lamiri sun ce gwamnatin shugaba Bush ba ta kokarin da ya kamata na mayar da harkokin tsaro a hannun ’yan iraqi, kuma ba ta matsa lamba kan sabbin shugabannin Iraqi da su yi gyara ga tsarin mulkinsu domin kara shigar da ’yan Sunni da mata cikin gwamnati.

XS
SM
MD
LG