Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al-Qa'ida Ta Ce Ita Ce Ta Kai Harin Da Ya Ci Tura Kan Matatar Mai Mafi Girma A Duniya


Wani sakon da aka buga a wani dandalin kungiyar al-Qa’ida a duniyar gizo ya dauki alhakin harin da aka yi yunkurin kaiwa jiya jumma’a da nufin fasa matatar mai mafi girma a duk duniya, wadda take yankin gabashin Sa’udiyya.

Wannan sako na al-Qa’ida, wanda ba a tabbatar da sahihancinsa ba, ya bayyana harin a zaman wanda yayi nasara, ya kuma ce mahara bam din sun samu shiga cikin yankin da aka dauki tsauraran matakan tsaronsa a kewayen matatar man.

Hukumomin Sa’udiyya sun ce an wargaza wannan harin a lokacin da masu gadi suka bude wuta a kan motoci guda biyu na maharan, wadanda suka yi bindiga. An ce an kashe masu gadi biyu da mahara biyu a wannan lamari. Ministan mai na Sa’udiyya ya ce bindigar da motocin maharan suka yi ba ta shafi ayyuka a matatar ba, wadda take samar da kashi biyu bisa uku na man kasar.

Farashin mai ya tashi sama da fiye da dala biyu kan ganga guda a bayan da aka samu labarin harin na Sa’udiyya, kasar da take zaune a kan rubu’in dukkan danyen man fetur da aka tabbatar da shi a duniya.

XS
SM
MD
LG