Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firayiministan Kanada ya roki shugaba Karzai ya kare Abdul Rahman daga kisa


Firayi ministan kasar Canada Stephen Harper yace shugaban kasar Afghanistan Hamid karzai ya fada masa cewa Ba-afge nan da aka yanke masa hukunci kisa saboda yayi ridda, ba za’a kashe shi ba. Mr. Harper yace ya kira shugaban Afghanistan din a wayar tarho shekaranjiya Laraba domin ya nuna damuwarsa game da ran Abdul Rahman wanda yake jiran hukuncin kisa. Firayiministan Canadan ya ce Mr karzai ya fada masa cewa za’a hanzarta tsaida shawara akan yadda za’ayi da Abdel Rahman. Tun da fari ran Alhamis da safe, sakatariyar harkokin wajen Amirka Condelizza Rice ta roki Mr. Karzai akan ya sassautawa Abdel Rahman.

Wata sanarwa da wani mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amirka ya bayar, tace Mrs. Rice ta fadawa shugaba Karzai cewa Amirka tana goyon bayan‘yancin walwalar yin duk addini da mutun yake son yi. Ranar Laraba kuma shugaba Bush na Amirka yace hankalinsa ya tashi sosai game da wannan al’amari na Abdul Rahman, sannan ya ce zai matsawa shugaban Afghanistan lamba akan ya ceto ran Abdul Rahman.

XS
SM
MD
LG