Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijeriya Ta Yarda Zata Mikawa Liberiya Tsohon Shugaba Charles Taylor


Nijeriya ta yarda zata mikawa hukumomin Liberiya tsohon shugaba Chales Taylor, wanda yake zaman gudun hijira a Nijeriya.

Gwamnatin Nijeriya ce ta bayyana wannan cikin wata sanarwar da ta bayar asabar din nan. Ba a san ko yaushe ne zata mika shi ba.

Wata kotun dake samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya mai zama a kasar Saliyo ta tuhumi Mr. Taylor da aikata laifuffukan yaki. An ba shi mafaka a Nijeriya a shekarar 2003, domin taimakawa wajen kawo karshen yakin basasar shekaru 14 a Liberiya.

Tun fari, shugabar kasar Liberiya, Ellen Johnson-Sirleaf, ta roki shugabannin Afirka da su yarda su mika Taylor ga kotun mai bin kadin laifuffukan yaki domin ta yi masa shari'a.

Sanarwar da gwamnatin Nijeriya ta bayar ta ce hukumomi sun ki yarda da kiraye-kirayen mika Mr. Taylor ga kotun ta musamman a saboda yin hakan zai keta yarjejeniyar da ta sa tsohon shugaban yayi murabus daga kan kujerarsa.

Nijeriya ta nace a kan cewa zata mika Mr. Taylor ne kawai ga gwamnatin da aka zaba ta hanyar dimokuradiyya a kasar Liberiya idan har ita gwamnatin ta bukaci haka.

XS
SM
MD
LG