Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Atiku Yace shugaban Obasanjo ne, ba mataimakinsa ba ne  ya kamata ya sauka daga gadonsa na mulki.


A karon farko, mataimakin shugaban Nigeria ya fito fili ya nuna adawarsa ga shirin ta-zarce. A ranar Alhamis ne Atiku Abubakar ya bayyana rashin yardarsa da wannan shirin a lokacinda yake jawabi ga wani taron manyan shugabannin siyasar Nigeria dake adawa da yiwa kundin tsarin mulkin Nigeria gyaran fuska don chanja wa’adin mulki biyu da ya tanada. Daga baya ne mataimakin shugaban ya gayawa sashen Hausa na VOA cewa a dukkan alamu akwai shirin da ake na “neman wa’adi na ukku”, saboda haka yake kira akan ‘yanmajalisar dokokin tarayya da su zo su hada kai da wadanda basa kaunar wannan shirin don a bata shi.

Koda yake a can kwanan baya shugaba Obasanjo ya gayawa VOA cewa shirin ta zarce “baya cikin muhimman abubuwan dake gabansa a yanzu”, an san cewa bai yanke kaunar cewa zai iya neman a kara mishi wa’adi na ukku ba. Wani kakakin shugaba Obasanjo ya yi kira akan mataimakin shugaban da cewa sai yayi murabus don kuwa, a cewar kakakin, in dai har zai zauna yana sukar lamirin gwamnatin, bai kamata ace yana cikinta ba.

To amma kuma Garba Shehu, jami’in hulda da kafofin watsa labarai na mataimakin shugaban kasa, bai bata lokaci ba wajen maido da murtani, yana cewashima shugaba Obasanjo sai yayi murabus. Yace shugaban ne, ba mataimakinsa ba, ya kamata ya sauka daga gadonsa na mulki.

XS
SM
MD
LG