Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin 'Yan Shi'a Na Iraqi Sun Yarda Za Su Tsayar Da Babban Dan Siyasa, Jawad al-Maliki, A Zaman Firayim Minista


Shugabannin 'yan mazhabin Shi'a na Iraqi sun ce babbar gamayyar jam'iyyun Shi'a ta yarda zata tsayar da babban dan siyasa, Jawad al-Maliki, a matsayin firayim minista.

Gamayyar ta cimma wannan yarjejeniya yau Jumma'a a Bagadaza, a wani yunkuri na warware cikasdin da aka yi makonni ana fama da shi a kan wanda zai rike wannan mukami.

A baya, 'yan siyasa na mazhabin Shi'a sun zabi firayim minista mai ci, Ibrahim al-Jaafari, domin ya ci gaba da rike wannan matsayi a sabuwar gwamnatin da za a kafa, amma sai Kurdawa da 'yan mazhabin Sunni suka bayyana adawarsu da nadin nasa, su na masu fadin cewa bai dauki matakan kwarai ba na kawo karshen tashin hankali a kasar.

Jiya alhamis, Malam al-Jaafari ya bayyana shawarar janyewa a wani yunkurin kawo karshen wannan sabani. Al-Maliki jigo ne a jam'iyyar al-Jaafari ta Da'awa.

A wani labarin kuma, wani kwamandan sojojin Amurka a Iraqi, wanda ke jawabi ga 'yan jarida a hedkwatar ma'aikatar tsaron Amurka ta wayar tauraron dan Adama, ya bayyana fatar cewa samun ci gaban siyasa a Iraqi zai tauye karfin 'yan tawaye.

Kanar Davis Gray ya ce idan aka ci gaba da zama babu gwamnati, 'yan tawayen za su kara kokarin gurgunta tsarin siyasar da haddasa rarrabuwar kawuna.

XS
SM
MD
LG