Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Madugun 'Yan Tawayen Chechnya, Shamil Basayev


Babban jami'in tsaron kasa na Rasha, ya ce an kashe madugun 'yan tawayen Chechnya, Shamil Basayev, a jamhuriyar Ingushetia dake kudancin kasar.

A lokacin wani taron da suka yi cikin fadar Kremlin wanda aka nuna a gidan telebijin na Rasha, babban jami’in leken asiri na Rasha, Nikolai Patrushev, ya fadawa shugaba Vladimir Putin cewa an kashe Shamil Basayev cikin dare lokacin wani farmaki na musamman a jamhuriyar ta Ingushetia mai iyaka da Chechnya.

Mr. Patrushev ya ce, "an samu nasarar kaddamar da wannan farmakin ne a saboda irin rawar da ’yan leken asirin Rasha dake kasashen waje suka taka wajen bin sawun makamai da ake jigilarsu zuwa Rasha, kuma an kashe wasu ’yan tawaye da dama a wannan farmaki."

Shugaba Vladimir Putin ya bayyana kashe madugun ’yan tawayen na Chechnya a zaman sakamakon da ya dace "...a saboda yaran da suka rasa rayukansu a Beslan da kuma wasu hare-haren da ya kitsa cikin Rasha a ’yan shekarun nan." A cikin watan Satumbar 2004, wasu ’yan bindiga sun mamaye wata makaranta a garin Beslan dake Ossettia ta Arewa. Akwai mutane fiye da dubu daya cikin makarantar a lokacin. An zub da jini a karshen wannan mamaya inda aka kashe mutane 331, fiye da rabinsu yara kananan.

Shamil Basayev ya dauki alhakin kai wannan farmaki da kuma wasu da dama a cikin Rasha inda daruruwan mutane suka mutu. Basayev ya jagoranci yin garkuwa da mutane masu dimbin yawa na farko a garin Budyonnvsk dake kudancin Rasha a 1995, ya kuma yi ikirarin cewa shi ne ya kitsa mamaye wani dakin wasa na Moscow da aka yi a 2002, inda mutane 129 suka mutu.

Babban jami’in leken asirin Rasha Nikolai Patrushev ya ce ’yan tawayen sun yi fatar kara matsin lambar siyasa a kan shugabannin Rasha a lokacin taron kolin kasashen duniya masu arzikin masana’antu da za a yi nan gaba cikin wannan mako a birnin St. Petersburg, amma kuma bai yi karin haske ba.

Majiyoyi na kusa da askarawan Chechnya ba su yi sharhi nan take a game da rahoton da Rasha ta bayar na mutuwar Basayev ba.

XS
SM
MD
LG