Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sandan Pakistan Sun Sake Yi Ma Benazir Bhutto Daurin Talala


'Yan sandan Pakistan sun sake yi ma shugabar 'yan adawar kasar, Benazir Bhutto, daurin talala cikin daren litinin, a yayin da kungiyar kasashe renon Ingila, Kwamanwels, ta bada Pakistan wa'adin kwanaki goma kan ta dage dokar-ta-bacin da ta kafa, ko a dakatar da ita.

Tsohuwar firayim ministar ta yi shirin jagorancin wani gangami yau talata daga birnin Lahore zuwa birnin Islamabad domin matsa lamba a kan shugaba Pervez Musharraf ya maido da yin aiki da tsarin mulkin kasa, ya kuma yi murabus daga kan mukamin babban hafsan sojojin kasar. Amma babban baturen 'yan sanda na Lahore, Aftab Cheema, ya ce an haramta yin gangami da kuma zanga-zanga a karkashin dokar-ta-bacin, kuma 'yan sanda sun samu bayanin sirri na wata makarkashiyar kai hari a wurin gangamin.

Hukumomi sun girka ma'aikatan kurkuku da daruruwan 'yan sanda a kewayen gidan da Mrs. Bhutto take zaune ciki.

Ministocin harkokin wajen kasashen Kwamanwels dake yin taro a London, sun bai ma Pakistan wa'adin zuwa ranar 22 ga watan nan na Nuwamba kan ta maido da yin aiki da tsarin mulki, ta kuma dage dokar-ta-baci, ko kuma dai a dakatar da ita. Sakatare-janar na kungiyar, wadda ta kunshi Britaniya da kasashen da ta yi musu mulkin mallaka, Don McKinnon, ya kuma ce tilas gwamnatin Musharraf ta kawar da tarnakin da ta yi ma 'yan jarida, ta kuma kirkiro da yanayin gudanar da zabe ba tare da ha'inci ba.

Litinin da maraice, kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya ambaci ofishin jakadancin Pakistan a London yana fadin cewa Pakistan ba zata yanke wata shawara bisa la'akari da wa'adin da wasu zasu ba ta daga wajen kasar ba.

XS
SM
MD
LG