Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Barack Obama Da Hillary Clinton Su Na Yakin Neman Zaben Karshe...


Masu neman jam’iyyar Democrat ta tsaida su takarar kujerar shugabancin Amurka, Barack Obama da Hillary Clinton, su na yakin neman zabe gadan-gadan yau litinin, jajiberen muhimman zabubbukan tsaida dan takara guda biyu da za a yi gobe talata.

Abokan hamayyar, kuma sanatoci, sun yi yakin neman zabe sosai a jihohin Indiana da Carolina ta Arewa kafin zabubbukan.

A cikin hirar da aka yi da ita daga Jihar Carolina ta Arewa yau litinin da safe, Hillary Clinton, ta kare kalamun da ta yi cewar idan ita ce shugaba, Amurka zata kaddamar da abinda ta kira "martani mai tsanani" a kan Iran idan ta kai hari kan Isra’ila da makaman nukiliya.

Obama ya soki Uwargida Clinton a saboda ta ce zata “shafe” Iran daga bangon duniya idan ta kai hari kan Isra’ila. A lokacin da yake magana da gidan telebijin na CNN daga Indiana, Obama ya ce irin wadannan kalamu na tsokana ne, kuma kalamu ne irin wadanda shugaba George Bush yake amfani da su. Yace zai maida martani da karfi ne shi idan Iran ta kai irin wannan harin.

Kuri’un neman ra’ayoyin jama’a sun nuna Obama yana gaban Clinton a Jihar Carolina ta Arewa, yayin da suke kunnen doki a Jihar Indiana.

XS
SM
MD
LG