Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masana Sun Ce Ana Iya Rigakafin Sulusin Dukkan Cutar Sankara


Masana suka ce a duniya, babu wani abinda ke haddasa cutar sankara da ake iya rigakafinsa kamar taba sigari. Taba tana haddasa mutuwar kashi 80 zuwa kashi 90 cikin 100 na dukkan masu mutuwa a sanadin sankarar huhu. Haka kuma, taba ita ce take haddasa mutuwar kashi 30 cikin 100 na dukkan masu mutuwa a sanadin cutar sankara a kasashe masu tasowa, ciki har da sankarar makogwaro da ta ciki.

Kwararru sun ce rungumar dabaru masu fadi da nagarta, kamar haramta yin tallar taba sigari a kafofin labarai, da kara kudin harajin da ake sanyawa kan taba da tallafawa masu shan taba wajen dainawa, zasu iya rage yawan masu shan tabar a kasashe da dama.

Kasidar da Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya, WHO, ta dauka kan dakile taba sigari, wadda aka amince da ita a watan Mayu na 2003, tana kokarin rage yawan mutanen dake mutuwa ko suke kamuwa da cututtuka a dalilin shan taba sigari.

Sauya irin abincin da ake ci da yadda ake ci ma wata hanya ce mai nagarta ta rage cutar sankara. Akwai alaka a tsakanin kiba da wasu cututtuka na sankara kamar sankarar makogwaro, da ta dubura da ta nono da kuma ta koda. Abincin da yake da ‘ya’yan itatuwa da ganyayyaki mai yawa yana iya kare jiki daga kamuwa da cututtuka da dama na sankara.

A wani gefen kuwa, yawaita cin jan nama, da naman da aka sarrafa shi (kamar wanda aka daka aka gauraya da wasu abubuwan adana abinci), su na kara kasadar kamuwa da cutar sankara ta dubura. Haka kuma, cin abinci mai kyau, da cin abinci ta yadda ya kamata domin rage kasadar kamuwa da cutar sankara, su na kuma taimakawa wajen rage kasadar kamuwa da cutar zuciya.

Motsa jiki a kai a kai da gujewa yin kiba sosai tare da cin abinci mai kyau, sukan hadu su rage kasadar kamuwa da cutar sankara sosai.

XS
SM
MD
LG