Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Afirka Ta Yamma Zasu Yi Taron Koli Kan Guinea-Conakry


Shugabannin kasashen Afirka ta Yamma sun yarda zasu yi taron koli cikin wannan makon domin tattauna tankiyar siyasar da ta ke akwai a kasar Guinea-Conakry. Za a yi wannan taron kolin ranar asabar a Abuja, babban birnin Nijeriya, a ranar da ita ma Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka ta shirya ganawa domin tattauna yiwuwar kafa takunkumi a kan gwamnatin mulkin soja ta kasar Guinea.

An yi Allah wadarai da gwamnatin ta mulkin sojan Guinea, hagu da dama, a saboda wutar da sojojinta suka bude a kan masu zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati a ranar 28 ga watan Satumba.

Majalisar Dinkin Duniya, MDD, da wata kungiyar kare hakkin bil Adama ta kasar sun ce an kashe mutane dari da hamsin da bakwai. Gwamnati Guinea ta ce mutane hamsin da bakwai na kai kawai aka kashe, ta kuma ce akasarinsu an tattake su ne suka mutu lokacin da mutane ke ribibin fita daga filin wasan Conakry, babban birnin kasar.

Jiya talata, titunan babban birnin sun kasance wayam a rana ta biyu ta yajin aikin gidan kowa da shi da aka shirya domin tunawa da wadanda aka kashe. Kungiyoyin kwadago ne suka shirya wannan yajin aiki na kwana biyu domin jimamin wadanda suka mutu.


XS
SM
MD
LG