Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Addini Sun Kaddamar Da Gagarumin Shirin Yaki Da Zazzabin Cizon Sauro, Malariya, A Nijeriya


Shugabannin addini a Nijeriya sun kaddamar da wani gagarumin yunkurin da ba a taba yin irinsa ba, wanda kuma zai ci tsabar kudi dala miliyan dubu daya, domin dakile cutar zazzabin cizon sauro, ko maleriya, wadda ke kashe mutane har dubu 300 kowace shekara a Nijeriya kawai.

Wannan gangamin shugabannin addini da aka sanyawa suna "Faith United for Health", ya hada kan shugabannin Musulmi da na Kirista a fadin Nijeriya, kuma yana kokarin raba gidajen sauro har guda miliyan 63 ga gidaje fiye da miliyan 30 a Nijeriya nan da karshen shekarar 2010.

Haka kuma, gangamin zai horas da malaman addini su dubu 30 kan yadda za su yada sakonnin rigakafin kamuwa da cutar maleriya a Nijeriya.

Wakili na Musamman na babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya mai kula da yaki da Cutar Maleriya, Ray Chambers, ya halarci bukin kaddamar da wannan gangami a Abuja, har ma ya ce, "Ta hanyar yin aiki tare, shugabannin addini na Nijeriya su na da gafaka, da tasiri da kuma zarafin isar da sako a kowane lungu na kasar cewa gidajen sauro su na ceton rayuka.

Ya kara da cewa, "Kokarin nasu zai taimaka wajen tabbatar da cewa yaran Nijeriya masu tahowa zasu kasance masu koshin lafiya da karfin jikin da za su iya tsunduma gadan-gadan cikin harkokin kyautata rayuwarsu."

Ofishin Chambers ya bayar da sanarwar cewa tabbatar da samun kayayyakin yaki da cutar maleriya a Nijeriya nan da karshen 2010, kamar gidan sauron da aka jika da magani, da fesa magungunan kashe sauro a cikin gidaje da kuma samar da magunguna masu nagarta ga wadanda suka riga suka kamu da cutar, za su taimaka wajen cimma gurin Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya na tabbatar da cewa nan da shekara ta 2015, babu mutumin da zazzabin cizon sauro ko maleriya ke kashewa a duniya.

XS
SM
MD
LG