Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Filayen Jiragen Sama A Duniya Sun Kara Matakan Tsaro...


Filayen jiragen sama a fadin duniya su na kara tsaurin matakan tsaron da suke dauka dangane da jirage masu zuwa Amurka, a bayan da wani dan Nijeriya wanda yayi ikirarin cewa yana da alaka da kungiyar al-Qa’ida, yayi kokarin tayar da bam a cikin wani jirgin da ya taso daga Amsterdam zuwa birnin Detroit a nan Amurka.

Fasinjoji a cikin wannan jirgin da ya taso ranar Kirsimeti, sun ce sun ji wata kara, suka kuma ga hayaki a lokacin da Umar Farouk Abdul Mutallab mai shekaru 23 da haihuwa yayi kokarin tayar da nakiya ba tare da nasara ba kafin jirgin ya fara yiwowa kasa dab da zai sauka. Nan da nan sauran fasinjoji da ma’aikatan jirgin suka taru suka danne shi.

Hukumomin Amurka sun bukaci kamfanonin safarar jiragen sama da su kara daukar matakan tsaro kan dukkan jiragen da zasu taho Amurka. Ita ma Nijeriya ta bayar da umurnin binciken lamarin.

Wasu rahotanni sun ce Mutallab ya daure wata hoda a kafarsa domin gaurayawa a cikin wani sirinji na allura dake dauke da wani irin ruwa. Dan majalisar wakilan Amurka, Peter King, wani babban dan kwamitin tsaron cikin gida na majalisar, yace jami’ai ba su taba ganin irin wannan nakiya ba. Yace Mutallab yana da alaka da kungiyar al-Qa’ida.

Wani dan majalisar wakilan Amurka dabam, kuma babban wakili a kwamitin kula da ayyukan leken asiri na majalisar, Pete Hoekstra, yace Mutallab yana da hulda da masu tsananin kishin Islama a kasar Yemen.

Gidan telebijin na ABC ya ambaci wani bayanin da aka yi ma jami’an tsaro na cewa Umar Faruq Abdul Mutallab, dalibi ne mai koyon aikin Injiniya a wata jami’a a kasar Britaniya, kuma yayi ikirarin cewa a kasar Yemen aka ba shi wannan nakiya.

Jami’an tsaro sun ce Mutallab ya kone sosai a jikinsa, kuma an kama shi a lokacin da jirgin ya sauka.

Jami’an Amurka su na yi masa tambayoyi.

Wannan jirgi na kamfanin Northwest Airline da Delta ya sauka lafiya a filin jirgin saman Detroit dauke da fasinja 278. Wasu daga cikinsu sun ji rauni amma maras muni.

Kakakin fadar White House, Bill Burton, ya ce shugaba Barack Obama ya bayar da umurnin da a dauki dukkan matakan da suka dace domin kara tsaron zirga-zirga ta sama. Burton yace Mr. Obama yana sa idanu kan lamarin daga Hawaii, inda yake hutu tare da iyalinsa.

Jami’ai suka ce Umar Faruk Abdul Mutallab ya taso ne daga Nijeriya, kuma koda yake akwai sunansa cikin wasu bayanai na hukumomin leken asirin Amurka, an ce babu sunansa a cikin jerin mutanen da gwamnatin Amurka ba ta yarda su shiga wani jirgin sama ba. Jami’an kasar Netherlands suka ce ya isa filin jirgin saman Schipol na Amsterdam cikin wani jirgin ne dabam.

XS
SM
MD
LG